Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masarautar Zazzau Ta Mika wa Gwamna El Rufai Sunayen Mutum Uku - Rahotanni


Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris
Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris

Rahotanni daga Najeriya na cewa Masarautar Zazzau ta aikawa da Gwamna Nasiru El Rufai sunayen mutum uku daga cikin mutum 11 da suka nuna sha’awarsu ta maye gurbin Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris da ya rasu.

Sarkin ya rasu ne a ranar Lahadi bayan da ya kwashe shekara 45 akan karagar mulkin masaruatar. Ya rasu yana da shekara 84.

Daga cikin mutum ukun na farko ya samu maki 89, na biyu ya samu maki 87 sannan na uku ya samu maki 53 a mizanin da aka auna su, kamar yadda wata majiya a masarautar ta tabbatarwa Muryar Amurka.

Ko da yake wasu kafafen yada labarai sun bayyana sunayen mutum ukun da aka fitar.

Amma majiyar ta tabbatar da cewa lallai an tara sunan mutum Uku.

Wasu kafofin yada labarai sun ce mutum takwas ne suka nuna sha’awar darewa karagar mulkin masarautar.

A halin da ake ciki kallo ya koma fadar gwamnatin jihar ta Kaduna wacce ke arewa maso yammacin Najeriya yayin da rahotanni ke cewa ana can ana wani zama tsakanin gwamna El Rufai da masu zabar sarki.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG