Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sabon Sarkin Biu


Jama'a sun yi cincirindo tare da daukar matakan kandagarki a wurin nadin sabon Sarkin Biu, Mai Martaba Mustafa Umar Mustafa.

An nada Mai Martaba Mai Mustafa Umar Mustafa a matsayin sabon sarkin Biu, bayan rasuwar mahaifinsa Alh. Mai Umar Mustafa Aliyu a wani Asibitin Gwamnatin tarayya dake garin Gombe, a shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Mai Martaba Mai Mustapha Umar Mustafa shine sarki na 29, kuma shine babban da ga maihaifinsa, marigayi Alh. Mai Umar Mustapha.

Nadin Sabon Sarkin Biu
Nadin Sabon Sarkin Biu

An nada sabon sarkin ne a fadar masaurautar Biu, bayan da Sakataren gwamnatin jihar Borno, Alh. Usman Jidda Shuwa ya mika masa wasika, tare da rakiyar Mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur.

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG