Gwamnatin Afghanistan da Kungiyar Taliban Sun Yi Hasarar Rayuka a Yankin Helmad

Dakarun Amurka dake taimakawa Sojojin Afghanistan

Ana cigaba da yawan fadace fadace tsakanin 'yansandan gwamnatin Afghanistan da 'yan kungiyar Taliban dake kokarin sake kwace kasar gaba daya

Jami’an kasar Afghanistan sun ce a kalla ‘yan Sandan tsaron kan iyaka guda 22 da mayakan kungiyar Taliban guda 35 ne suka mutu a wata mumunar arangamar da ta barke a yankin Helmand dake Kudancin kasar.

Haka kuma jami’an tsaron Afghanistan da dama ne suka jikkata a wasu fadace-fadacen a gundumar Nawzad, inda watanni biyu kenan da ‘yan Taliban ke rike da wajen.

Har ila yau mayakan sa kan sun kuma kwace ikon muhimman wurare na gundumar Musa Qala dake yankin na Helmand. Wannan na faruwa ne bayan da jami’ai ke ikirarin sun fatattaki ‘yan Taliban daga yankin.

‘Yan Taliban din sun kasa iya jurewa wajen kare inda suka kwace ikonsa na tsawon lokaci. A ranar Talata ma sun bada sanarwar janyewa gaba daya daga birnin Kunduz da ke arewacin kasar, wajen da suka kwace ikonsa na tsawon wasu kwanaki.