Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sojan Amurka Ya Fadi A Afghanistan


FILE - Sojojin Afghanistan na layi domin hawa wani jirgin su mai kirar C-130 a filin saukar jirage na Kandahar, Afghanistan, 18 Agusta, 2015.
FILE - Sojojin Afghanistan na layi domin hawa wani jirgin su mai kirar C-130 a filin saukar jirage na Kandahar, Afghanistan, 18 Agusta, 2015.

Wani jibgegen jirgin sama mai jigilar kaya kirar C-130 na sojan Amurka ya fadi a filin jirgin saman Jalalabad na kasar Afghanistan.

Abinda ya janyo halakar mutane akalla 11. Da misalin karfe 12 na daren jiya ne wannan hatsarin ya faru kuma har zuwa yanzu ba’a ce ga abinda yake shine sanadin fadowar jirgin ba.

Kafofin soja dake filin jirgin saman Bagram a can Afgaistan sunce wadanda suka mutu a hatsarin sun hada da sojan Amurka shidda dake aiki a cikin jirgin, hade da wasu fararen hula biyar dake aiki da NATO.

Kungiyar Taliban tayi ikrarin cewa mayakanta ne suka kakkabo jirgin da bindigoginsu amma wani hafsan sojan Amurka, Major Tony Wickman ya karyata haka, yana cewa suna da tabbacin cewa ba wani mataki da abokan gaba suka dauka ne ya janyo fadowar jirgin ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG