Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Taliban Na Son Mayarda Hannun Agogo Baya a Afghanistan


Wasu fursinonin da 'yan Taliban suka sako daga gidaan yarin Kunduz
Wasu fursinonin da 'yan Taliban suka sako daga gidaan yarin Kunduz

A wani mugun farmaki da ba'a taba gani ba a Afghanista mayakan Taliban sun kutsa cikin babban birnin Kunduz suka kwace ikon garin tare da kafa tutarsu

Mayakan Taliban a Afghanistan sun kwace ikon garin Kunduz bayan mummunan harin da suka kai yayinda suka keta cikin birnin dake arewacin kasar.

Karon farko da ‘yan tawayen zasu kwace wani babban gari, tun bayan hambarar da mulkinsu a shekarar 2001.

Sannan sun saki fursunoni da yawa daga kurkukun birnin. Shedun gani da ido sun ce, da sassafe ‘Yan Taliban din suka kai farmaki kan garin suka kuma kafa farar Tutarsu a dandalin taskiyar birnin.

Hukumomin Afghanistan sun ce rundunar Sojojinsu sun isa Kunduz da shirin kai harin sake kwatar ikon garin daga mayakan na Taliban.

Kakakin Ma’aikatar cikin gidan Afghanistan Sediq Sediqi, ya fadawa Muryar Amurka cewa, tuni har Sojojinsu sun hallaka ‘yan ta’adda fiye guda 25.

Ya fadi cewa ba wani jami’in tsaron da ya rasa ransa, amma jaridu sun rawaito mutuwa da raunata wasu ‘yan sandan gwamnati da dama.

XS
SM
MD
LG