Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Afghanistan da Mayakan Taliban Na Gwabza Kazamin Fada a Kunduz


Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani

Dakarun Afghanistan dake samun kariya ta sama daga sojojin Amurka sun gwabza kazamin fada da mayakan Taliban a kokarin kwato birnin Kunduz

An gwabza kazamin fada kusa da tashar saukar jiragen sama dake birnin Kunduz, lokacin da sojojin Afghanistan wadanda dakarun Amurka na sama suka rufawa baya, suka kaddamar da hari da niyyar sake kwato birnin daga hanun 'yan tawayen Taliban, wadanda suka kama garin dake arewacin kasar, tun ranar Lahadi.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid, da mazauna Kunduz sun gayawa Muryar Amurka cewa, an fara gwabza fadan ne a daren jiya Talata kusa da tashar jiragen saman ne, bayan da mayakan Taliban suka kaddamar da wani kazamin hari kan tashar jiragen saman, inda sojojin Afghanistan din suka fake ranar Litinin. Rahotanni sun ce wani gefen tashar yana hanun 'yan Taliban ahalin yanzu.

Jami'an gwamnatin kasar basu ce komi ba kan fadan da ake gwabzawa a baya bayan nan.

Tunda farko ma'aikatar tsaron kasar tace jami'an tsaronta ciki harda sojoji na musamman sun fara kai hare hare a wuren da mayakn Taliban din suke a safiya r jiya Talatan da zummar kutsawa cikin garin. Ma'aikatar tace jiragen yakin Amurka sun kai hari kan 'yan Taliban bayan ma'aikatar ta nemi taimakon su.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG