Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Gumurzu Wajen sake kwace Garin Kunduz a Afghanistan


Yanzu haka dai ana kan gumurzu a cikin birnin Kunduz

Dakarun kasar Afghanistan sun sake kwace birnin Kunduz dake arewacin kasar daga mayakan Taliban da asubahin yau alhamis, bayan wani kazamin gumurzu bisa ga cewar jami’ai.

Abdul Rauf Ibrahimi, kakakin majalisar wakilai ya shaidawa manema labarai a birnin Kabul cewa, dakarun gwamnati suna kara kutsawa a Kunduz, sai dai bai bayyana ko sun kwace birnin ba ko babu.

Yace yanzu haka dai ana kan gumurzu a cikin birnin Kunduz, kuma yana da wuya a san bangaren birnin dake karkashin ikon gwamnati da bangaren da har yanzu yake hannun abokan gaba.

Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida Sediq Sediqqi ya shaidawa Muryar Amurka cewa, dakarun Afghanistan sun kaddamar da hari cikin dare da ya yi nasara.

Mazauna garin Kunduz sun shaidawa manema labarai yau da asuba cewa, birnin yana karkashin ikon dakarun tsaron gwamnati.

Sai dai Taliban da ta kwace ikon birnin ranar Litinin tace har yanzu yana karkashin ikonta.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG