Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hari Kan Asibbitin Kunduz a Afghanistan Kuskure Ne - Janar Campbell


Janar John Campbell yayinda yake bada shaida a majalisar dokokin Amurka kan harin na Kunduz
Janar John Campbell yayinda yake bada shaida a majalisar dokokin Amurka kan harin na Kunduz

Wani babban kwamandan mayakan Amurka a Afghanistan, Janar John Campbell yace dakarun Amurka ne suka kai hari bisa kuskure kan wani asibiti a birnin Kunduz, a farmaki da suka kai da jiragen yaki, har mutane 22 suka halaka.

Janar na mayakan sojojin-kasan, ya gayawa wani kwamiti na majalisar dokokin Amurka cewa, sojojin Afghanistan ne suka nemi taimakonsu, saboda 'yan Talibana sun kai musu farmaki daga ginin asibitin wanda yake karkashin kulawar kungiyar aikin jinkai da ake kira Doctors without Borders.

Janar Campbell wanda shine babban kwamandan dakarun NATO a Afghanistan, yaki ya bada wani karin haske dangane da farmakin, domin acewarsa a hukumomin Amurka dana Afghanistan suna ci gaba da gudanar da binciker kan harin.

A fadar White House, kakakinta Josh Earnest, ya kira harin da cewa "mummunan hadari, wanda Amurka take daukar batun da dukkan muhimmanci da ya dace".

Kungiyar ta Doctors without Borders, ta yi Allah wadai da harin da ya halaka ma'aikatanta 12, da marasa lafiya 10, a zaman wani mummunan matakin keta dokokin kasa-da kasa.

Shugabar kungiyar Joanne Liu, ta fada jiya talata cewa, wannan ba lamari ne "da za'a mance dashi bane a zaman kuskure, ko abunda ka iya faruwa a fagen yaki".

Tace hadin guiwar da Amurka da Afghanistan suke yi, yana nufin sun "hada baki su rusa asibiti mai aiki sosai, har tana cewa "wannan tamkar amsawa sun aikata laifin yaki ne.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG