Yayin ziyara da ya kai majalisar dokokin Kano gwamnan ya tattauna da 'yan majalisar akan mahimmancin 'yan jam'iyyarsu ta APC su samu hadin kai domin kawar da kungiyar Boko Haram da duk wani aikin ta'adanci.
Yaki da 'yan Boko Haram ko ta'adanci ba na shugaban kasa ba ne kawai. Kamata ya yi su hada kai domin a samu a kawar da matsalar.
Furucin na gwamna Imo ya sa masana harkokin tsaro da shari'a suka yi tsokaci akan kwamitin nan na gwamnonin arewa da suka dorawa alhakin zakulo masu tallafawa 'yan kungiyar ta Boko Haram da wasu dake aiwatar da ta'adanci musamman a arewa maso gabashin Najeriya.
Keften Abdullahi Adamu Bakoji mai ritaya yace a ganinsa harkar tsaro shi ne a sallamawa jami'an tsaro shi zai kawo mafita. Babu yadda gwamnoni zasu iya zakulo masu tallafawa 'yan ta'ada sai sun hada da jami'an tsaro. Jami'an tsaro sun san yawancin abubuwa. Sun san 'yan siyasa. Sun san 'yan ta'ada. Idan an basu dama zasu zakulosu ba sai gwamnoni sun wahalar da kansu ko bata dukiyar jama'a ba.
Shi kuwa Barister Audu Bulama Bukarti cewa ya yi idan an yi la'akari da dokokin Najeriya ta'adanci al'amari ne da ya shafi kasa baki daya. To duk abun da za'a yi ya zama karkashin shugaban kasa da kuma gwamnatin tarayya. Batun zakulo wadanda suke tallafawa ta'adanci dokar 2013 ta yi bayani dalla dalla inji Barrister Bukarti. Ita ma hukumar EFCC akwai ikon da dokar ta bata dangane da kudaden ta'adanci. Barrister Bukarti yace saboda haka idin gwamnoni nada wata shawara da zata taimaka kamata ya yi su rubutawa shugaban kasa wasika su yi bayani.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5