Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabbatar da Ingantaccen Tsaron Kasa Ne Kan Gaba - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Jiya Alhamis a Abuja Shugaba Buhari ya sake jaddada tabbatar da ingantaccen tsaro a matsayin abun da gwamnatinsa ta fi maida hankali a kai

Shugaba Buhari yace gwamnatinsa ta fi mayarda hankalinta akan tabbatar da samun ingantaccen tsaro saboda idan babu tsaro rayuwa da harkokin tattalin arziki ba zasu yiwu ba.

Yayinda yake jawabi lokacin da ya karbi bakuncin hafsan hafsoshin kasar Birtaniya Janar Nicholas Houghton shugaba Buhari ya sake nanata jajircewar gwamnatinsa na kawo karshen ta'adancin Boko Haram cikin gaggawa.

Yace "Kafin a gudanar da mulkin kasa dole ne a tabbatar da tsaro domin rayuwa da zamantakewar jama'a da duk wani kokarin inganta tattalin arziki ba zasu yiwu ba cikin yanayin rashin tsaro"

Shugaban ya cigaba da cewa "Dole a tabbatar da yanayin tsaro kafin a fara sake gina kasa. Kawo yanzu Najeriya nada 'yan gudun hijira miliyan day da dubu dari biyar da rigingimu suka rabasu da muhallansu. Dukansu suna bukatar a mayar dasu gidajensu.

Makarantunsu da asibitocinsu da mijami'unsu da masallatansu da gonakansu da duk wata hanyar rayuwarsu 'yan ta'ada sun lalatasu. Idan ba'a kula dasu ba zasu karaya su juyawa gwamnatin kasar baya.

Yayinda aka samu aka kawar da Boko Haram kuma an samu yanayin dake da ingantaccen tsaro rayuwa zata koma yadda take da. Wannan shi ne burinmu kuma abun da muke kokarin yi ke nan. Sai mun cimma wanan burin ne wasu ayyuka kamar su aikin noma, harkokin tattalin arziki da zamantakewar jama'a na yau da kullum zasu kankama. 'Yan Najeriya mutane ne masu kuzari da hazaka" inji Shugaba Buhari a cikin kalamun da ya yiwa hafsan hafsoshin Birtaniya.

Shugaban Najeriya yace Najeriya ta yaba da goyon bayan da Birtaniya tke bata ta hanyar sake horas da dakarun kasar kana ya sake neman karin taimako a wasu bangarorin kamar tsarin shirye shiryen yaki da kayan yaki da kuma bayanan siri.

Ya sake kiran kasashen duniya da su taimakawa kokarin kasashen yankin tafkin Chadi domin inganta tsaro a yankin tekun Guinea da masu satar man fetur din Najeriya ke bi suna fita dashi zuwa waje.

A nashi jawabin Janar Houghton yace shugabancin Buhari wani babban dama ne Najeriya ta samu na cigaba.

Janar Houghton yace ya yi farin ciki ganin irin cigaban da kasar ta samu a yakin da take yi da ta'adanci a karkashin shugabancin Shugaba Buhari. Ya tabbatarwa shugaba Buhari cewa Birtaniya zata cigaba da ba gwamnatin Najeriya goyon baya dangane da kokarin da ta keyi na kawo karshen ta'adancin Boko Haram.

Janar Houghton yace "Zamu kuma taimaka mu tabbatar cewa duk abubuwan dake haddasa ta'adanci an kawar dasu. Ban da samun nasara ta hanyar soji muna kuma son kasar ta dore ta tsaya daram"

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG