Yayin da wa’adin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin Najeriya na murkushe Bako Haram ke kara karatowa, masana na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu kan fa’idar wa’adin da kuma yiwuwar cima ma buri kafin cikar wa’adin ko kuma akasin hakan. Wannan kuwa na zuwa ne bayan da sojojin Najeriya su kaba da ‘yan Boko Haram wa’adin mika wuya ko kuma su fuskanci bugun kwab daya yayin da su ke kara samun nasara kan ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Wani masanin harkar tsaro a Najeriya mai suna Dr. Bawa Abdullahi Wase ya ce yawancin lokaci idan aka ji sojoji na gargadi da kuma ba ta wa’adi ko kashedi to sun shirya ne kuma sun gane cewa sun a iya yin nasara. Y ace wannan gargadin na da muhimmanci saboda zai iya ba da dama ga wa’adanda aka rinjaya zuwa cikin kungiyar su iya ficewa.
Wakilinmu da ya aiko wannan rahoton ya kuma lura cewa watsi da kananan sojoji da ake yin a kawo matsala wajen kokarin yaki da ‘yan Boko haram saboda ana karya masu gwiwa. Don haka ya yi kira ga hukumomi da su dau matakan tabbatar da cewa na ba da karfin gwiwa ga kananan sojoji musamman tunda su ne aka fi turawa fagen daga. To saidai babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Manjo-Janar Tukur Burutai ya ce yanzu za a magance matsalolin da su ka addabi sojojin Najeriya a yakinsu da Boko Haram.