Nan take ‘yan sanda suka dora alhakin harin da aka kai a garin Baga Sola kan kungiyar Boko haram mai tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama.
‘Yan sanda da jami’an asibiti sun ce a kalla mutane hamsin kuma suka ji raunuka sakamakon hare haren da aka kai a garin dake takfin Chadi.
Janar Banyaman Cossingar yace an dana daya bom din ne a kasuwar kifi, yayinda aka dana sauran biyu a sansanan ‘yan gudun hijira dake bayan garin.
Makon da ya gabata, hukumomi suka ce mayakan kungiyar Boko Haram sun yi arangama da sojojin kasar Chadi kusa da tafkin Chadi. Wata majiyar soji tace an kashe sojoji goma sha daya da mayaka sha bakwai a musayar wutar.
Kasar Chadi tana daya daga cikin manyan kasashen dake bada gudummuwa a rundunar hadin guiwa da aka kafa ta yakar kungiyar Boko Haram wadda ta fara kai hare hare kasashen dake makwabtaka da Najeriya da suka hada da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar, banda Najeriya inda kungiyar ta sami asali