Janar Gowon ya bayar da shawarar ne a wata budaddiyar wasika da ya aikewa shugabannin kasashen yammacin nahiyar Afrika dake karkashin kungiyar ECOWAS a yau Laraba yana mai cewa matakin da kasashen 3 suka dauka zai yi mummunar tasiri ga al’ummar kasashen yammacin nahiyar Afrika din wadanda suke cin moriyar hadin gwiwar kasashen dukka.
Janar Gowon ya kuma jadada kiran shi ga shuwagabannin kasashen ciki, da wadanda ke karkashin mulkin soja, su ajiye bambance-bambancen dake tsakaninsu su hada gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaito a yankin.
Dattijo Gowon ya kuma bukaci dukkan shuwagabannin kasashen kungiyar ECOWAS 15 din su shirya wa halartan wani babban taro domin tattauna makomar al'ummarsu, tsaro da zaman lafiyar yankin da kuma rawar da kasashen duniya za su taka idan aka yi la'akari da yanayin siyasa da ake ciki a halin yanzu.
Kungiyar ECOWAS wacce aka kafa a shekarar 1975 mai mambobi 15 a matsayin babbar hukumar siyasa da shiyya ta yammacin nahiyar Afirka, mai muradin inganta dunkulewar tattalin arziki a kasashen mambobinta a shekarun baya-bayan nan na ta fama wajen kawo karshen mamayar da sojoji suka yi a yankin, ciki har da kasar Mali a shekarar 2020, Burkina Faso a shekarar 2021, sai Nijar a shekarar 2022.
Mambobin kungiyar ECOWAS wato kasashe 15 ban da mambobi hudu da aka dakatar tun bayan da suka koma karkashin mulkin soja wato Burkina Faso, Guinea, Mali da Nijar, tare da mambobi takwas na kungiyar Tattalin Arziki da Lamuni na Afirka ta Yamma, sun amince da rufe dukkan iyakokin kasar da Nijar, tare da dakatar da hada-hadar kudi da kuma rufe kadarorin kasar a bankunan kasashen waje.
Saidai daga baya kasashen uku, wadanda suka kifar da gwamnatin hadin kan yankin Sahel kan ECOWAS bayan hambarar da gwamnatin dimokaradiyya a Nijar, sun sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, 2023.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a yankunan Ouagadougou, Bamako da Yamai ta shugabannin sojojinsu, Capt. Ibrahim Traoré na Burkina Faso, Kanal. Assimi Goita na Mali da Brig. Janar Abdourahamane Tchiani na Jamhuriyar Nijar sun sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS nan take.
Kasashen uku, wadanda a halin yanzu suke karkashin mulkin soja, sun ce sun fice da ga zama mambobin kungiyar ECOWAS saboda zargin kungiyar da kaucewa akidar shuwagabnnin da suka kafa ta da zimmar ci gaba da kishin nahiyar Afrika.
A saurari muryar tsohon Shugaban Najeriyar, Yakubu Gowon, yayin da ya karanta wasikar da harshen Ingilishi.
Your browser doesn’t support HTML5