Ghana Ta Rage Yawan Mace-Macen Mata Masu Juna Biyu Da Kashi 58%

Wannan ya kasa da burin ma'aikatar kiwon lafiya na rage mace macen da kashi 75% kamin 2015.

Darektan sashen kiwon lafiyar iyali na Ghana, Dr. Patrick Kuma-Abooagye, yace mata 740 ne suka mutuwa cikin mata dubu dari a lokacin haifuwa.Kasar ta kuduriyar anniyar ganin zuwa shekara ta 2015, kasar ta rage hakan zuwa kashi 75 cikin dari.

Duk da haka yace a kokarin da suka yi, yanzu an rage yawan mace macen da kashi 58% cikin dari, watau mata 3oo da yan kai ne suka mutuwa cikin wani dubu dari a lokacin haifuwa.

Dr. Aboagye, wand a ya bayyana haka a hira d amuka yi da shi cikin 'yan makon nin nan lokacin da wata tawagar masana kiwon lafiya daga Afirka suka kawo mana ziyarar anan Muriyar Amurka.

Dr. Patrick, ya aza nasarar da suka samu kan cikakken goyon baya da suka samu daga gwamnatin kasar, amfani da kungiyoyin raji kare lafiyar mata, da kuma bi-biya domin tabbatar komi yana tafiya cikin tsari.

Cikin kalubale da ma'aikatar take fuskanta wajen rage yawan mace-macen, sun hada harda jahilci,da talauci,da rashin wadatattun kayan more rayuwa, dana aiki, musamman a yankunan karkara