Bama-bamai sun tashi a wasu motoci biyu a Mogadishu, babban Birin kasar Somliya jiya Jumma’a, su ka hallaka mutane akalla 38, a cewar majiyoyin soji.
Dr. Abdulkadir Abdirahman Adam na sashin motocin daukar majinyata, ya ce an yi niyyar kai harin ne a Fadar Shugaban kasa da kuma wani otal. Mutane akalla 30 ne dai su ka ji raunuka. Adam yace akasarin wadanda abin ya rutsa da su fararen hula ne.
Fashewa ta farko ta auku ne daura da hedikwatar hukumar leken asirin tsaron kasar. ‘Yan mintoci daga bisani sai, sai wani bam din ya kuma tashi a wani wurin duba ababen hawa da ke a tazarar mita 300 daga Fadar Shugaban kasar Somliya.
Kungiyar al-Shabab ta yi ikirarin kai harin a wani bayanin da ta saka a yanar internet, inda ta ce ta auna harin ne kan jami’an gwamnati da kuma jami’an tsaro.
Facebook Forum