Wasu ‘yan kasar Congo guda biyar sun mutu yau dinnan Jumma’a, lokacin da ‘yan sanda da sojojin Rwanda su ka yi amfani da harsasan gaske wajen tarwatsa ‘yan gudun hijira, wadanda suka shafe kwanaki uku a harabar ofishin Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da ‘Yan Gudun Hijira da ke Yammacin Rwanda.
Wata takardar bayanin da ‘yan sandan kasar Rwanda suka fitar tace, “sun yi amfani da irin karfin da ya dace, wanda yayi sanadin jin raunuka ga masu zanga-zanga 20 da ‘yan sanda 7 da aka ruga da su zuwa asibiti. Sai dai kash! Guda biyar daga cikin masu zanga-zangar sun mutu daga bisani sakamakon raunukan da suka ji.”
‘Yan sandan sun ce sun kuma damke mutane 15 daga cikin masu zanga-zangar, wadanda suke zargi da gudanar da zanga-zanga ba bisa ka’ida ba, da yin garkuwa da mutane da kuma ingiza tashin hankali. ‘Yan gudun hijirar sun ce adadin wadanda su ka mutu na iya zarce adadin da ‘yan sanda su ka bayar.
A jiya Alhamis, Cibiyar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ko UNHCR a takaice, ta yi kiran da a kai zuciya nesa bayan da ta samu rahoton cewa, wata zanga-zangar da aka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Kiziba da ke kasar Rwandar ta rikide zuwa tashin hankali.
Facebook Forum