Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: CNDH Ta Yi Kira Ga Yiwa Dokar Haraji Garambawul


NIGER: Firayim Ministan Nijar a taron zaman lafiya
NIGER: Firayim Ministan Nijar a taron zaman lafiya

Hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH ta shawarci mahukuntan kasar jamhuriyar Nijar da su dauki matakan kawo gyara akan wasu tarin matsalolin dake haddasa cece-kuce a yanzu haka cikinsu har da dokar harajin 2018, wacce kungiyoyin fafutika ke ganin tayi tsauri ga masu karamin karfi.

A cewar kakakin hukumar CNDH, Talibi Musa, hukumar tayi wannan kira ne bayan lura da yadda tsarin kasafin kudaden shekarar 2018 wanda ke kokarin kawo rikici tsakanin kungiyoyin dake zanga-zangar nuna rashin amincewa da shi.

A daya bangaren kuma jam’iyyun kawance masu mulki da a karon farko sun fara tunanin fitowa kan tituna domin nunawa gwamnati cewa suna goyon bayan sabuwar dokar harajin. Hukumar dai na yin kira ga gwamnatin kasar Nijar ta ‘dauki matakan sanyaya zuciyoyin jama’a.

Hajiya Maryama Habibu, ‘daya daga cikin kwamishinonin CNDH, tace tun lokacin da ‘yan Majalisu suka saka hannu a dokar, ake ganin bangarori da dama suna fitowa suna nuna rashin amincewa da dokar. Ta kuma yi kira ga gwamnati da ta gyara abubuwan da suka kamata.

Hukumar kare hakin ‘dan Adama ta kasa dake Allah wa dai da masu amfani da shafukan sada zumunta don yada kalaman kabilanci, ta bukaci hukumar shari’ar Nijar ta ‘dauki matakan hukunta masu irin wannan mummunar akida dake barazana ga hadin kan jama’a.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG