Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Sun Sake Kauracewa Zabe a Kasar Djibouti


Ismael Omar Guelleh
Ismael Omar Guelleh

Har yanzu dai tsarin dimukuradiyya na tangal-tangal a kasar Djibouti, musamman ganin bangaren adawa ya sake kauracewa zabe a kasar.

Bayan kauracewa zaben Shugaban kasa na shekarar 2016, babbar jam’iyyar adawar Djibouti MRD, ta ce ba za ta shiga zaben Majalisar Dokokin da ake yi a yau Jumma’a ba a kasar, al’amarin dake kawo fargabar cewa tsarin Dimukuradiyya baya aiki a kasar ta gabashin Afrika.

“A Djibouti, akwai matsalar halacci, wato na tsarin dimukuradiyya da kuma matsalar halaccin Majalisar Dokoki saboda sam ba a gudanar da sahihan zabuka,” Kamar yadda Daher Ahmed Farah, shugaban jam’iyyar ta MRD ya gayawa Muryar Amurka. Farah yace gwamnati ta saba wa yarjejeniyar da aka cimma a karshen shekarar 2014, na kafa Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta.

Yace, muddun babu wata hukuma mai zaman kanta da zata sa ido kan harkar zabe, babu yadda za'a tabbatar da sahihancin tsarin zaben.“ Shiga zaben da ba'a yi cikin adalci, tamkar daurewa karya gindi ne. Saboda karya ce kuma jirwaye ne kawai mai kamar wanka.” Duk da nuna sha’awar sauye-sauye da ta yi, hobbasar Djibouti ta bangaren dimokaradiyya bata wadatar ba, a cewar Farah, saboda gwamnatin na murkushe adawa tana kuma takurawa ‘yan jarida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG