Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan ta Kudu Ta Na Tauye 'Yancin 'Yan Jarida


Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da suka yi binciken kwakwaf akan hakkin dan Adam a Sudan ta Kudu
Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da suka yi binciken kwakwaf akan hakkin dan Adam a Sudan ta Kudu

Binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a Sudan ta Kudu ya gano cewa gwamnatin kasar na tantance duk wani labarin da 'yan jarida zasu wallafa akan kasar tare da hana jama'a fadin albarkacin bakinsu tare da take hakkin mutane

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yace gwamnatin kasar Sudan ta Kudu naci gaba da tace duk wani labari da wata kafar yada labarai zata fitar tare da takaita 'yancin fadin albarkacin baki.

Rahoton mai taken ‘Yancin bayyana raayi da fadin albarkacin baki na kasar Sudan Ta Kudu’’

Yana gargadin da takaita damar bayyana raayi, wanda kuma wannan yana matukar tasiri ga ‘yan kassa, wannan yasa ake kara samun raguwar bayyana ra'ayi a kasar.

A cikin watanni 18 da suka shige, masu bincike na ofishin Ayyukan MDD dake kasar ta Sudan ta Kudu da na ofishin babban jami'in kula da 'yancin dan Adam na MDD dake kasar ta Sudan ta Kudu sun tattauna da wadanda aka ci ma zarafi, da wadanda suka ga abinda akayi ma wasu, da kuma 'yan rajin kare hakkin bil adama, dama ‘yan jarida a fadin kasar ta Sudan Ta kudu, inda aka tattara shaidar zarge-zargen take hakkin bil Adama har sau 99 a kasar.

Masu binciken a cikin wani bayani mai shafuka 30 da suka fitar cikin wannan satin, sun ce sun tabbatar da batutuwa har 60 dabam-dabam na tauye hakkin mutane har 102 na bayyana ra'ayoyinsu.

A wata yarjejeniyar tsagaita wutar da gwamnati da wasu masu ruwa da tsaki a kasar suka sanya wa hannu a cikin watan Disam,ba, musamman an haramta cin zarafin ma'aikatan kafofin yada labarai.

Babban jami'in MDD dake kasar Sudan Ta Kudu, David Shearer, ya shaidawa manema labarai a Juba babban birnin kasar a jiya alhamis cewa yawancin matakan take hakkin su na faruwa a yankunan dake hannun gwamnati, kuma da yawan wadanda wanna abin ya shafa ‘yan jarida ne.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG