Mbappe Ya Kai Faransa Ga Gaci

Mbappe yana murna da kocinsu Deschamps

Gabanin wannan wasa, an yi ta yamadidin cewa tauraruwar Mbappe mai shekaru 24 ta daina haskawa bayan da ya gaza zura kwallo ko daya a wasannin hudu da PSG ta buga.

Dan wasan Faransa Kylian Mbappe, ya taimakawa kasar wajen samun nasara shiga gasar zakarun turai bayan da ya zura kwallaye biyu a ragar Netherland.

Faransa ta lallasa Netherland da ci 2-1 a rukuninsu na B.

Gabanin wannan wasa, an yi ta yamadidin cewa tauraruwar Mbappe mai shekaru 24 ta daina haskawa bayan da ya gaza zura kwallo ko daya a wasannin hudu da PSG ta buga.

Sai dai wadannan kwallaye da ya zura a wannan karawa ta rufe baki mutane da dama.

Mbappe ya zura kwallon farko a minti na bakwai sai kuma ta biyu a minti na 53.

Dan wasan Dutch Quilindschy Hartman ya farke kwallo daya a minti na 83.

A gefe guda kuma Girka ta doke Ireland da ci 2-0 nasarar da ta saka ta a mataki na biyu bayan Faransa a rukunin.

A ranar Litinin Netherland za ta fafata da Girka.