An dauki dan wasan mai shekaru 31 da haihuwa a kan abun daunkar marasa lafiya a farkon rabin lokaci na biyu a filin wasa na Parc des Princes a ranar Lahadi, bayan ya samu rauni a kafarsa ta dama.
Kungiyar PSG ta yi nasara da ci 4-3, sakamakon bugun firinkit da Lionel Messi ya yi a muntunan lokacin da aka kara na karshe, amma raunin da Neymar ya ji ya haifar da damuwa, musamman ma wasan zagaye na biyu na ‘yan16 na gasar cin kofin Zakarun Turai da za su yi da Bayern Munich a ranar 8 ga watan Maris mai zuwa.
Christophe Galtier ya ce Neymar, wanda ya shirya kwallon farko da Kylian Mbappe ya ci kuma ya ci wa PSG kwallo ta biyu, kuma yanzu PSG ta tabbatar ya gurde a kafarsa.
Duk da haka, za a bukaci karin gwaje-gwaje don sanin ko akwai wata matsala a mahadar kashinsa.
“Wadanda ya samu rauni a idon sawu yayin wasan da suka buga da Lille, Meymar an yi masa MRI a ranar Lahadi,” in ji wani bayanin likitocin PSG.
“Wannan bai bayyana karaya ba. Za a gudanar da wani sabon gwaji a cikin sa’ao’i 48.”
Nuno Mendes shi ma an cire shi saboda rauni a wasan Lille, tare da dan wasan Portugal dan yana fama da wani karamin kumburi a gwiwarsa ta dama.