Yau Asabar Paris Saint Germain za ta kai wa Nice ziyarar inda za su kara a gasar Ligue 1 ta Faransa.
Wasan na zuwa ne bayan da PSG ta sha kaye a wasanni biyu a jere lamarin da ya sa tagomashinta ya yi kasa.
Yayin da wasu masoya kwallon kafa ke cewa tawagar ‘yan wasan za ta je da fushi ne wasu kuwa cewa suke za su je wasan ne kamar zakaran da ruwan sama ya buga.
PSG ta sha kaye a wasanni takwas a dukkanin gasar da take bugawa.
Wasan da Nice na kuma zuwa ne yayin da kungiyar ta PSG ke fuskantar suka daga dan wasanta Kylian Mbappe, wanda ya nuna fushinsa kan yadda kungiyar take tallata shi.
Mbappe ya ce yana ganin ba daidai ba ne mahukuntar kungiyar su rika tallata shi shi kadai a kungiyar duba da cewa PSG tawaga ce da ta kunshi ‘yan wasan da suke matukar ba da gudunmowa matuka.
Mutane da dama sun yaba da yadda Mbappe ya yi wa Neymar da Messi kara da ya fito ya kalubalanci hukumomin kungiyar ta PSG.
Hakan kuma na faruwa ne yayin da tauraruwar Messi take dishewa a kungiyar inda a baya-bayan nan magoya bayan PSGn suka yi masa ele.