Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, da yake magana a Tel Aviv sa'o'i bayan ya gana da Netanyahu, ya ce har yanzu yana ganin "akwai yiwuwar cewa, za a cimma yarjejeniya" kuma ya gargadi Shugaban Isra'ila game da matakan da ya dauka da yin maganganu da za su kara rura wutar rikicin.
Netanyahu ya shaidawa wani taron gidan talabijin cewa, ya umarci sojoji da su "shirya yin aiki" a Rafah, kuma watanni kalilan su ka rage Isra’ila samu nasara kan Hamas.
A birnin Beirut, wani babban jami'in Hamas ya mayar da martani, yana mai cewa "nacin Netanyahu da ci gaba da kai hare-hare ya ba da tabbacin cewa dama manufar ita ce kisan kare dangi ga al'ummar Palasdinu".
Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su da aka sako a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da aka kulla a watan Nuwamba ita ma tana matsa wa shugaban na Isra'ila lamba.
Adina Moshe ta fadawa wani taron manema labarai a Tel Aviv, yayin da take aika sako ga Netanyahu cewa, "Komai yana hannunka,".
"Kai ne. Kuma ina matukar jin tsoro da matukar damuwa cewa, idan ka ci gaba da wannan nacin na ruguza Hamas, za a rasa sauran mutanen da aka yi garkuwa da su," in ji ta.
Tun da farko, wakilin Amurka Blinken, a rangadinsa na biyar a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar yakin, ya bayyana fatan ganin an tsagaita wuta da kuma sako wadanda aka yi garkuwa su, duk da cewa ya yi gargadin cewa, akwai sauran aiki a gaba .
"Amma mun maida hankali sosai kan yin wannan aikin kuma muna fatan samun damar a sako da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su," in ji Blinken bayan ganawa da Netanyahu a birnin Kudus.
A yanzu haka dai ana ci gaba da gwabza yakin da ya shiga wata na biyar a zirin Gaza da Hamas ke mulki, inda ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce a cikin sa'o'i 24 da suka gabata an kashe akalla mutane 123, yayin da 'yan jaridun AFP suka bayar da rahoton karin hare-haren bama-bamai mai tsanani a garuruwan kudancin kasar.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya firgita da rahotannin da ke cewa, sojojin Isra'ila za su shiga yankin Rafah da ke cike da fiye da rabin al'ummar Gaza.
Sojojin Isra'ila sun ci gaba da kutsawa a kudancin yankin gabar teku, inda aka gwabza fada mafi muni a birnin Khan Yunis a cikin 'yan makonnin nan.