Farashin Wasu Daga Cikin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa

Bisa Kididdiga da mujallar Sport Business ta yi, ya nuna cewa kungiyoyin kwallon Kafa na kasar Ingila masu buga Firimiya lig sun kashe zunzurutun kudi har fam miliyan £150 a ranar karshe da aka rufe hada hadar saye da sayarwar ‘yan wasan kwallon Kafa na duniya a watan janairu.

An sayi ‘yan wasa kamar su Pierre-Emerick Aubameyang daga Borussia Dortmund zuwa Arsenal £56m, Lucas Moura, Paris St-German zuwa Tottenham £23m, Olivier Giroud Arsenal zuwa Chelsea £18m.

Andre Ayew West Ham, zuwa Swansea £18m, Badou Ndiaye Galatasaray zuwa Stoke City £14m, Jordan Hugill Preston zuwa West Ham £10m, Da kuma wasu ‘yan wasan da aka bada aron su.

Hakan ya bada jimillar kudin da aka kashe na sayen ‘yan wasa kimanin fam miliyan £430 a cikin watan janairu daga farko zuwa karshenta. Dan wasan da yafi tsada a wannan cinikayya a watan janairu shine mai tsaron baya Virgil van Dijk, daga Southampton zuwa Liverpool, akan kudi fam miliyan £75m.

Shi kuwa Shugaban hukumar kula da kwallon Kafa ta duniya FIFA, Infantino, ya nuna "damuwarsa sosai" game da yawan kuɗin da "ke gudana daga masana'antar kwallon kafa" zuwa cikin kudaden wakilai (Agents)

Daga karshe ya ce a shekara ta 2016/17 kungiyoyin 'yan wasan Ingila sun ba da fam miliyan £174m ga wakilan ‘yan wasa kawai a cikin cinikin da akayi. Shugaban ya ce "Dole ne mu magance wannan batu, dole ne a bude labule," Inji Infantino "Ina damuwa sosai game da yawan kudaden da ke gudana daga kamfanonin kwallon kafa".

Your browser doesn’t support HTML5

Farashin Wasu Daga Cikin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa