Kocin kungiyar Manchester united Jose Mourinho, ya sanya hannu kan Karin kwantiraginsa a kungiyar har zuwa shekarar 2020, tare da karin wasu shekaru a nan gaba.
Mourinho mai shekaru 54 da haihuwa wanda ya zo Manchester united ranar 27 ga watan Mayu, 2016 zai karkare kwantiragin sa a shekarar 2019 yanzu kuma sai 2020, ya ba hukumar gudanarwa ta kungiyar karkashin jagorancin Shugabanta Edward Woodward bisa zabensa cewar shine manaja a wannan babban Kulob.
Shugaban kungiyar kwallon Kafa ta PSG Nasser Al-Khelaifi, ya yi alkawarin sayar da dan wasan kungiyar Neymar, mai shekaru 25, a shekara mai zuwa ga kungiyar Real Madrid amman da sharadin cewar sai dan wasan ya jagoranci Kulob din na PSG wajan lashe kofin zakarun nahiyar turai.
Neymar, ya zo kungiyar Paris Saint-Germain a farkon kakar wasan bana daga Barcelona, akan zunzurutun kudi har yuro miliyan £222 inda ya kasance mafi tsada a duniyar kwallon Kafa.
Borussia Dortmund, ta fara ja da baya akan batun Olivier Giroud, daga Arsenal, amma Pierre-Emerick Aubameyang, zai iya shiga Arsenal akan farashin fam miliyan £56.
Dan wasan gefe na kungiyar PSG Lucas Moura da shugaban Kungiyar kwallon Kafa ta Tottenham Daniel Levy, sun sadu a ranar Alhamis dan tattaunawa kan batun dawowarsa kungiyar.
Kocin kungiyar Leicester City, Claude Puel yace ba zai saida dan wasan gaban sa Riyad Mahrez, a wannan watan janairun ba duk da kasancewar kungiyoyi da dama sun nuna shi'awarsu ta ganin sun dauke dan wasan a watan nan.
Facebook Forum