Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kula Da Wasannin Lig-Lig Ta Kasa Ta Ci Wasu Kungiyoyi Tara


Hukumar kula da wasannin lig ta tarayyar Najeriya LMC ta ci tarar kungiyoyin kwallon Kafa guda uku da suka fafata gasar Firimiya lig ta kasar (NPFL).

Kungiyoyin sune Heartland Owerri, wadda aka ci tarar kudi Naira Miliyan guda #1,000,000, sakamakon rashin tsaro a wasan da suka buda da Sunshine makon farko na NPFL na bana inda aka tashi babuci 0-0, hakan ya kawo hayaniya da aka kasa shawo kanta a filin wasa na Dan Anyiam dake Owerri.

Sai kuma kungiyoyin Katsina United, da kuma Kano Pillars, a wasan farko na gasar ta Firimiya lig ta ban wnda aka yi a Filin wasa na Muhammadu Dikko inda aka tashi 2-2, anci tarar Katsina united, tarar kudi Naira miliyan #1,000,000, sakamakon rashin tsaro a filin.

Ita kuma Kano Pillars dubu dari bakwai da hamsin #750,000, sakamakon magoya bayanta sunyi jefe jefe da lalata wasu muhimman abubuwa wadanda suka hada da kujerun zama da kofofi da taga dake filin yayin wannan wasa.

Bayan haka Hukumar LMC ta basu damar nan da awowi 48 in basu amince da hukuncin ba su daukaka kara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG