A yanzu haka kungiyoyin kwallon Kafa daban daban musamman na nahiyar turai na ta kokarin kammala cinikayya ‘yanwasan kafin lokacin rufewar. Ga kuma wasu daga cikin kasuwancin da ya kammala da wada ake kokarin kammala wa.
Kungiyar kwallon Kafa ta Arsenal ta kammala cinikin danwasan gaba na kasar Gabon Pierre Emerick Aubagmeyang, daga kungiyarsa ta Borussia Dortmund akan kudi fam miliyan £60.
Inda ya kasance danwasa mafi tsada wace kungiyar ta Arsenal ta taba saya a tarihinta. Aubameyang mai shekaru 28 ya zo kungiyar Borussia Dortmund ne a shekara 2013 daga Saint Etienne akan kudi fam miliyan £13.
Ya kasance danwasan da yafi kowa zura kwallaye a raga a gasar Bundesliga na kasar Jamus a shekaru da suka wuce, inda a bana danwasan ya jefa kwallaye 21 a wasanni 24 da ya buga. Wasansa na karshe da kungiyar ta Dortmund shine ranar Asabar da ta wuce wadda suka canjaras sa Freiburg.
Tuni dai kungiyar ta Borussia Dortmund ta cimma yarjejeniya wajan dauko danwasan gaba na Chelsea Batshuayi a matsayin aro domin ya maye gurbinsa.
Ita kuwa Chelsea ta amince da ta saye danwasan Arsenal Olivier Giroud akan kudi fam miliyan 18, har ila yau Chelsea ta kammala sayen danwasan baya na Roma Emerson Palmieri, akan kudi fam miliyan 23.
Kungiyar kwallon Kafa ta Manchester city ta kammala sayen danwasan baya na Athletic Bilbao maisuna Aymeric Laporte akan kudi fam miliyan £57, Inda ya kasance danwasan da yafi kowane danwasan tsada a kungiyar tun bayan da ta saye Kevin De bruyne fam miliyan £55 2015.
A 2017/18 Manchester city ta saye ‘yanwasa masu tsaron baya guda 5 wanda kudin su ya haura fam miliyan 200.
Facebook Forum