Fadar shugaban Amurka ta fada jiya litinin cewa shugaba Donald Trump “bai yarda da duk zarge-zargen da wata mai wasan fina-finan batsa, Stormy Daniels ta yi na cewa ya kwana da ita sau daya a shekarar 2006 ba," kuma shekaru 5 daga baya aka yi mata barazana akan ta yi shiru gameda wannan alakar.
Wani mai magana da yawun Trump, Raj Shah yayi watsi da batun cewa Trump yayi wani laifi, saboda babban lauyansa, Michael Cohen, ya biya mai wasan fina-finan batsar dala 130,000 “kudin toshiyar baki” daga aljihunsa jim kadan bayan zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2016.
“Kudaden diyyar zarge-zargen karya ba a kotu ake biyansu ba,” a cewar Shah, wanda manema labarai suka yi mai caa da tambayoyi, bayan wata doguwar hira da aka yi da Stormy Daniels a tashar talabijin din CBS shekaranjiya Lahadi, a wani shirin turanci da ake kira “60 Minutes”, hirar da ta janyo ‘yan kallo mafi yawa a cikin shekaru 10.
Mr. Shah ya kuma yi watsi da ikirarin Daniels na cewa a shekarar 2011, a lokacin da ta ke kan hanyar zuwa wajen motsa jiki a Las Vegas da ‘yar jaririyar diyarta, wani mutum da ba ta taba gani ba yayi mata barazana.