Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Za ta Maida Martani Akan Korar Jami'anta 60 Daga Amurka


Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov

Lavrov ya dora laifin korar jami’ai dayawa akan matsin lamba daga Amurka.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fada yau Talata cewa gwamnatin kasarsa zata maida martani akan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na korar jami’an diflomasiyyar Rasha su 60 daga Amurka cikin mako daya, bisa zargin leken asiri.

Wasu kasashe 22, ciki harda Faransa, da Jamus, da Poland, su ma sun kori jami’an leken asirin Rasha 77, a cewar fadar shugaban Amurka. Amma banda kasar Australia cikin kasashen, wadda ta sanar yau Talata cewa zata kori jami’an leken asiri 2 da ba a bayyana ko su waye ba.

Matakin da Amurka ta dauka, tare da rufe wani karamin ofishin jakadancin Rasha a kasar, maida murtani ne akan Rasha, gameda abinda ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta kira keta yarjejeniyar makaman guba da kuma saba dokar kasa-da-kasa, abinda ya hada da harin gubar da aka kai kan wani tsohon jami’in leken asirin Rasha da diyarsa a Burtaniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG