'Yan wasan kwallon kwando na Amurka daga kungiyoyin da ake kira Celtics daga birnin Boston, da kuma Sacremento Kings, wadanda suke babban birnin jahar California sun hada kai jiya Lahadi gabannin su fara wasa, suka yi zanga zanga kan yadda 'yan sanda suka harbe suka kashe wani bakar fata wanda baya rike da makami.
'Yan wasan sun saka riguna da aka rubuta “A nuna adalci dukan mu daya ne”. A bayan rigunan kuma aka rubuta sunan matashin #StephenClark.
Clark ya rasa ransa ne ranar 18 ga watan nan a Sacreento. 'Yan sanda suna zargin yana fasa motoci yayi sata, da suka tunkare shi, nan suka harbe shi sau 20, suna zaton yana da bindiga,amma daga bisani aka samu woyar celula ce a hanunsa.
Magajin garin Sacremento ya bukci da a gudanar da cikakken bincike.
Ahalinda ake ciki kuma,Allah Ya yiwa Linda Brown rasuwa, mutuniyar da yayinda take karama tayi suna domin sunanta ne kan karar da ta kai har kotun kolin Amurka, wanda hukuncin da kotun ta yanke a shari'ar data shiga tarihi, da ake kira Brown V. Board of Education a 1954 ta kawo karshen wariyar launin fata a makarantun Amurka.
Ta bar duniya tana da shekaru 76.
Facebook Forum