Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Wasu Kasashe Sun Kori Jami'an Diflomasiyar Rasha Su 137


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Jiya Litinin Amurka ta kori jami'an diflomasiyar Rasha su 60 daga kasarta bisa zargin karya dokokin kasa da kasa kana wasu kasashen duniya suka yi hakan ta korar wasu 77

A jiya Litinin, Amurka ta kori jami'an difilomasiyyar Rasha su 60 wadanda take zargin 'yan leken asiri ne da su fice daga kasar nan da mako daya. Akalla wasu kasashe 23 ciki harda da Faransa, da Jamus, da Poland, sun kori fiyeda jami'an "leken asiri" na Rasha 137, kamar yadda Fadar White House ta tabbatar.

Matakin da Amurka ta dauka tare da rufe wani karamin ofishin jakadancin Rasha dake birnin Seattle martani ne kan abunda ta ce "mummunar keta yarjejenyar hana amfani da makaman guba, da kuma karantsaye data yiwa dokokin kasa-da-kasa" ta wajen amfani da makaman guba wajen kaiwa wani dan leken asirin Rashan mai fuska biyu tareda da 'yarsa da hukumomin kasar dake Moscow suka yi a Britaniya, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi bayani.

Rahotanni suka ce shugaban na Amurka wanda ya yi magana makon jiya da shugaban Rasha Vladimir Putin, shi ya dauki shawarar korar jami'an difilomasiyyar.

Firayim Ministar Britaniya Theresa May, ta yi marhabin lale da martani da aka tsara, tana mai cewa wannan mataki da kawayen mu suka dauka ya nuna cewa mun tsaya tare kafada-da kafada, wajen aikewa da sako mai karfin gaske ga Rasha cewa ba zata ci gaba ta keta dokokin kasa da kasa ba.

Hukumomin Rasha suka ce Shugaba Vladimiri Putin zai yanke shawara kan irin martani d a Moscow za ta yi kan wannan mataki.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG