Kasuwar sayar da hannayen jari ta Amurka ta hau sama sosai a jiya Litinin, bayan da 'yan kasuwa suka daina ko suka rage tsoron za'a yi fito-na fito tsakanin Amurka da China ta fuskar ksuwanci.
Kasuwar da aka fi sani da Dow Jones wacce aka sawa ido sasssanta daban daban har 30 sun cira da kashi daya da rabi a hada hadar d a aka yi a farkon bude kasuwar jiya, yayinda wasu sassan kasuwar suma suka bi sawu.Kasuwnnin hannayen jari a Asiya sun tashi hadin gambiza, amma a turai kasuwannain sun nosa.
Kasuwannin kasashen duniyar sun yi warwas a makon jiya, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bada sanarwar zai kakabawa China haraji kan kayayyaki da take shigo da su Amurka da kudinsu ya kai dala milyan dubu 60
Facebook Forum