Tashoshin sun hada da Channels, AIT, da kuma Arise News. Saboda haka za a sa musu takunkumi har sai sun biya tara da ya kama daga Naira miliyan 2 zuwa 3.
Mukaddashin Babban Darekta na Hukumar Kula da Kafofin yada labarai ta NBC, Farfesa Armstrong Idachaba ya yi bayani cewa an ci tarar wadannan gidajen talabijin din daga Naira Miliyan 2 zuwa 3 ne saboda laifin kin bin ka'idojin yada labarai na kasar.
Hukumar ta NBC ta ce an hukunta tashoshin ne domin yada hotunan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba na zargin harbe-harbe masu zanga zangar EndSARS.
Sakataren Kungiyar ‘yan jaridu na Najeriya, Shuaibu Leman, ya ce yin irin wannan hukunci ba daidai ba ne, su suna kallon matakin a matsayin wani yunkuri ne na musguna wa tashoshin talabijin din domin hana wa kafafen yada labarai ‘yanci a kasar.
Leman ya kara da ce idan an samu wata kafa ta yada labarai da laifi, kamata yayi a zauna akan tebur domin fayyace mata gaskiya da kuma nuna inda doka ta fara da kuma inda ‘yan cinsu ya tsaya kafin a dauki mataki.
Amma dan jarida mai zaman kansa, Bashir Baba, ya ce yana ganin hukuncin yayi daidai saboda ba su nuna kwarewa wajen bin ka'idar yin amfani da hotunan bidiyo da suka dauko kaitsaye ta kafafen sada zumunta ba.
Baba ya kara da cewa su wadannan dandula na sadarwa na zamani ko wane irin tarkace da suka hada da mutumin kirki da bata gari, kowa zai iya shiga ya yi abin da ya gama dama, sun je sun dauko hotunan bidiyo suka yada wa jduniya wanda ba a haka a aikin jarida.
Ita ma Kungiyar Kare Hakkin Tattalin Arziki ta SERAP ta yi tir da tarar da aka sanya wa gidajen talabijin din Channels, AIT da kuma Arise News, inda ta nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi hukumar NBC da ta daina tsoratarwa ko cin zarafin gidajen yada labarai masu zaman kansu.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5