Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gana Da Jonathan, Obasanjo, Gowon Da Sauran Manyan Kasa


Shugaba Buhari na gwanawa da tsofaffin shugabanin kasa.
Shugaba Buhari na gwanawa da tsofaffin shugabanin kasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kira tsoffin shugabannin kasar wani taron gaggawa don tattauna halin da kasa ke ciki.

Taron wanda ake yin sa ta yanar gizo a yanzu ya hada da tsoffin shugabannin kasa Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar, Yakubu Gowon da kuma Earnest Sohenkan.

Har ila yau taron ya hada da mataimakin shugaban kasa Prof Yemi Osibanjo da manyan hafsoshin sojin kasar da kuma hadiman fadar shugaban.

Mai bai wa shugaba Buhari shawara kan harkokin sabbin kafafen yada labarai Bashir Ahmad ya tabbatar da gudanar da taron a shafinsa na Twitter.

Taron na zuwa ne bayan jawabinsa jiya da yamma, na kokarin kwantar da hankalin 'yan kasa, akan zanga-zangar da ta janyo hankalin duniya, da jaddada wasu alkawura da zai maida hankali akansu.

Jawabin dai ya sha suka da kuma yabo, inda yayin da wasu ke yabawa wasu kuwa suna suka saboda bai tabo batun bude wuta da aka yi akan masu zanga zanga ba.

Wasu kuma suna cewa bai tabo batun harin ‘yan bindiga da aka kai a jihar Zamfara a kwanan nan ba wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 20.

An kwashe kusan mako biyu ana zanga zanga a sassan Najeriya inda ake kira da a rusa rundunar SARS da ke yaki da masu fashi da makami saboda gallazawa jama’a da suke yi.

Hukumomin kasar sun rusa rundunar suka maye gurbinta da wata da ake kira SWAT.

Zanga zangar ta kai ga asarar rayuka da barnata dukiyoyi da dama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG