Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Yi Warwason Kayan Tallafin Corona a Jihohin Najeriya


Yadda Jama'a suka yi warwason kayayyakin abinci a Yola, Adamawa
Yadda Jama'a suka yi warwason kayayyakin abinci a Yola, Adamawa

Matasa a wasu jihohin Najeriya, sun yi ta afkawa rumbunan adand abincin tallafin da gwamnati ta tanada don ragewa mutane radadin annobar coronavirus da ta addabi duniya.

Lamarin dai ya biyo bayan zanga zangar adawa da rundunar ‘yan sanda ta SARS da aka kwashe kusan mako biyu ana yi a sassan Najeriya, wanda a yanzu ya dan lafa bayan rusa rundunar ta SARS.

Duk da cewa zanga zangar ta lafa sosai, wani kalubale da ya kunno kai shi ne, yadda jama’a ke far wa rumbunan adana abinci na gwamnati suna kwasar kayan masarufi.

Cikin watannin da suka gabata, jihohin Najeriya da dama sun tanadi abincin da za a rabawa masu karamin karfi a lokacin da annobar COVID-19 ta barke a duniya – a wani mataki na rage radadin rashi da mutane suke fama da shi saboda zaman gida da aka yi.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto an far wa ire-iren wadannan rumbunan abinci a jihohin Legas, Filato, Taraba, Adamawa, Kaduna, Edo, Abuja, Kwara da sauransu.

Ko da yake, tun a lokacin ganiyar zanga zangar, an far wa wasu manyan wuraren kasuwancin masu zaman kansu ciki har da kona wasunsu lamarin da ya kai ga dumbin asarar dukiyoyi.

Legas

Kafofin yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito cewa jihar Legas da ke kudancin kasar na daga cikin jihohi na gaba-gaba da aka fara samun wannan salon afkawa rumbun adana abincin inda matasa suka far rumbun da ke Old Ojo Road da na Kirikiri Town da ke jihar suka yashe su baki daya.

Kayan da aka kwasa sun hada da wake, shinkafa, sukari, gishiri, man girki, taliya da dai sauransu.

Daruruwan mutanen da suka hada da yara da manya, mata da maza sun yi rububi a wuraren kamar yadda rahotanni da wasu bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta suka nuna, ko da yake Muryar Amurka ba ta da tabbacin wadannan hotunan bidiyo.

Gwamnatin jihar Legas ta ce dailin da ya sa aka yi jinkiri raba kayayya shi ne zanga zanga da ta barke dalili, kamar yadda mai taimakawa gwamna Babajide Sanwo-Olu kan harkar noma Abisola Olusanya ta fadawa jaridar Vanguard.

Tuni gwamnatin jihar ta Legas ta fara wani shirin tallafawa wadanda aka fasa shagunansu a jihar inda ta nemi 'yan kasuwar da lamarin ya shafa da su cika wani fom.

Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ita ma ta ayyana dokar hana zirga-zirga a wasu sassan jihar a ranar Asabar bayan da wasu da ta ce ba ta san ko su waye ba, suka farwa rumbun adana kayan masarufi da aka tanada don ragewa jama’a radadin annobar covid-19.

Wata sanarwa da Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Arwan ya wallafa a shafinsa na Twitter ta nuna cewa, an saka dokar ce a yankin Chikun da kuma kananan hukumomin da ke kudancin jihar.

“Wadannan yankuna sun hada da, Barnawa, Kakuri, da Television a kudancin Kaduna sannan sai Maraban Rido, Sabon Tasha, Narayi, Unguwan Romi da suke karamar hukumar Chikun.” Sakon Twitter ya nuna.

Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da “da yunkurin tunzura mutane da ake yi a kafafen sada zumunta na su ta da husuma.”

“Gwamnati na kira ga daukacin al’uma da su yi watsi da tunzura su da ake yi, su kuma gujewa duk wani da zai haddasa rudani ya kuma kawar da doka da oda.

A wata hira da Muryar Amurka ta yi da Aruwan, kwamishinan ya ce, “ba su san waye suka far wa wajen ajiyar abincin ba.”

Ya kuma ce sun dauki matakin ne a matsyain kandakari don kada ya jirkice ya koma tarzoma.

Da aka tambayi Aruwan dalilin da ya sa aka samu jinkirin raba kayayyakin sai ya ce, “wannan aiki da ake yi rukuni-rukuni ne kuma akwai fuskoki da yawa, da zaran an samu abu sai a raba, kuma dole ai sai an kimtsa. Saboda haka, duk wasu bayanai da ake yi ba gaskiya ba ne.”

Taraba

A karshen makon nan, gwamnatin jihar Taraba tabi sahun wasu jihohi wajen kafa dokar hana fita biyo bayan far ma wajen da aka adana kayayyakin tallafin na jihar da jama’a suka yi.

“Gwamnati ta yanke shawarar saka dokar hana fita a Jalingo, babban birnin jihar Taraba domin a maido da doka da oda.” Mukaddashin gwamnan jihar Eng. Haruna Manu ya ce bayan warwason kayayyakin da aka yi.

Sai dai duk da wannan doka jama'a sun sake fitowa da safiyar ranar Lahadi inda suka ci gaba da warwason.

“Sun fasa (rumbun) A.Y.A, sun fasa na Sakatariya.” Wani da ya shaida lamarin da ya nemi a sakaya sunansa ya fadawa wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ta wayar tarho.

Adamawa

Kamar jihar Taraba a jihar Adamawa da ke makwabtaka da ita, an samu irin wannan lamari inda tun da safe aka soma shiga wuraren ajiye kayayyakin tallafin da ke Kwanar Waya da kuma na Bakin Kogi.

“Nan Yola ne, ku zo ko kwashi kayan tallafi da ke Kwanar Waya.” Wata mata da ta kwashi kayayyakin ta fadawa Muryar Amurka tana haki.

Amma jami’an tsaro sun ce sun shawo kan lamarin.

“Gaskiya ne abin da ke faruwa a jihar Adamawa, tun da sanyin safiya, rundunar ‘yan sanda ta dauki matakai na tabbatar da zaman lafiya, sannan akwai masu shiga rumbun gwamnati suna kwasar kayayyaki, wannan abu ba daidai ba ne.” In ji Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar DSP Suleiman Yahya Nguroje.

Gwamnan Jihar Pilato, Samuel Lalong (Hoto: Twitter @PLSGov)
Gwamnan Jihar Pilato, Samuel Lalong (Hoto: Twitter @PLSGov)

“Duk wanda aka same shi da sabawa doka za a dauki matakin da doka ta tanada akansa.” DSP Nguroje ya kara da cewa.

Pilato

A jihar Pilato da ke tsakiyar arewacin Najeriya ma, daruruwan matasa ne suka fasa rumbunan adana abinci na gwamnati suka kwashe masara, dawa, taki da wassu kayayyaki da aka adana a hukumar samar da ruwa a jihar.

Matasan sun shafe yinin ranar Asabar suna gudanar da barnar da a yau Lahadi suka ci gaba da fasa ofisoshin ma’aikatun jihar Pilato da ta tarayya suna kwashe kayayyaki.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa a Jihar, Mr. Dan Manjang ya yi Allah wadai da lamarin yana mai cewa warwason ya hada har da shiga ofisoshin gwamnati ana kwashe kayayyakin.

Ana dai zargin hukumomin jihohi da boye kayayyakin tallafin, amma Manjang ya ce ba haka lamarin yake ba.

“Kayan Dangote da aka kawo an raba kowa ya gani na jihar Pilato ma an raba kowa ya gani, saboda haka, masu cewa gwmanati ta boye kayan ba su yi wa gwamnati adalci ba.”

Bayan aukuwar lamarin ne gwamnan jihar Pilato Simon Lalong ya sake sanya dokar hana yawo ta sa’oi 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu.

Gabanin wannan lamari, hukumomin jihar sun sassauta dokar da aka saka biyo bayan zanga zangar Endsars da aka yi a baya.

Abuja

Rahotanni daga Abuja babban birnin Najeriya ma na cewa wasu daruruwan mutane sun afkawa rumbun adana abincin gwamnati da ke Gwagwa-Karmo inda suka yi ta wawure su.

Jaridun Najeriyar da dama sun ruwaito cewa mutane da dama sun yi ta turuwar fita da buhuhhunan hatsi lamarin da ya janyo cunkoson abababn hawa yankin.

Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan sanda sun je sun tarwatsa dandazon jama’a yankin.

A dai ranar Juma’a ma makamancin wannan lamari ya faru a Ilori babban birnin jihar Kwara ya kuma faru a birnin Benin na jihar Edo da ma wasu sassan kasar.

Babu dai wasu bayanai da suka nuna cewa an kama wadanda ke da hannu a wannan warwaso na kayayyakin tallafin corona, amma hukumomin suna ikrarin suna gudanar da bincike, kuma duk wanda aka samu hannunsa a cikin zai fuskanci fushin hukuma.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG