Dubbai Sun Yi Maci Na Goyon bayan Putin A Moscow

Dubbai Sun Yi Maci Na Goyon bayan Putin A Moscow

Wannan gangami martani ne na zanga-zangar nuna kin jinin firayim ministan da 'yan hamayya suka yi ta shiryawa kafin zaben da za a yi.

Dubban magoya bayan firayim minista Vladimir Putin na kasar Rasha sun yi gangami yau alhamis a birnin Moscow.

Magoya bayan na Putin sun yi maci ta tsawon kogin Moscow kafin su hallara a filin wasa na Luzhniki dake kusa da nan, inda suka saurari jawabin da yayi musu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, yace Mr. Putin ya fadawa taron cewa shi ne zai samu nasara a zaben shugaban kasa da za a yi ranar 4 ga watan Maris, sai kuma ya juya ya tambayi wadanda suka hallara ko su na ganin zai yi nasara? Gaba daya filin wasan ya amsa da fadin cewa "Ehh" shi zai yi nasara.

Maci da kuma gangamin da ya biyo bayan martani ne ga zanga-zangar da aka yi ta gudanarwa a baya domin nuna kin jinin Mr. Putin, wanda ake tsammanin zai lashe wa'adi na uku kan kujerar shugabancin kasar Rasha a wata mai zuwa.

An faro zanga-zangar a watan Disamba a bayan da jam'iyyarsa ta United Russia ta ayyana nasara a zaben 'yan majalisar dokoki, koda yake ba da rinjayen da ta samu a can baya ba. 'Yan hamayya da 'yan kallo na kasa da kasa sun ce an yi magudi lokacin zaben, ciki har da cika akwatuna da kuri'un bogi.