Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kallon Zabe Sun Ce Putin Ya Yi Nasara Kamar Yadda Aka Tsara


Firai Ministan Rasha Vladimir Putin na zubar da hawaye a lokacin da ya ke ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasar da aka yi, a gaban dubban daruruwan magoya bayan shi da su ka yi dandazo a kofar Fadar shugaban kasar ta Kremlin
Firai Ministan Rasha Vladimir Putin na zubar da hawaye a lokacin da ya ke ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasar da aka yi, a gaban dubban daruruwan magoya bayan shi da su ka yi dandazo a kofar Fadar shugaban kasar ta Kremlin

Kungiyar tsaro da hadin kan Turai ta ce a zahirin gaskiya babu wata takarar da aka yi

‘Yan kallon zaben Turai sun ce ba wata-wata an tsara zaben shugaban kasar Rasha ne don a fifita Firai Minista Vladimir Putin wanda ya yi gagarumar nasarar da ba ta da tantama.

A cikin sanarwar da ta gabatar kungiyar tsaro da hadin kan Turai, ta ce a zahirin gaskiya babu wata takarar da aka yi. Ta ce yin amfani da arzikin gwamnati fiye da kima ya yayewa Putin duk wani shakkun kasa samun nasara a zaben.

Kungiyar tsaro da hadin kan Turai ta ce a bayyane ya ke an baiwa Putin wata damar fifiko ta yin amfani da kafofin yada labarai. Ta ce an takaitawa masu kada kuri’u damar su ta iya zabe tsakanin ‘yan takara masu yawa saboda ka’idojin rajista masu tsananin tsauri. Haka kuma kungiyar tsaro da hadin kan Turai ta bada rahotanni da daman a wasu abubuwan da ba su kamata ba da su ka faru a kashi daya cikin uku na rumfunan zabe.

Shugabannin hamayyar kasar Rasha sun shirya yin wata zanga-zanga Litinin din nan daf da Fadar Kremlin ta shugaban kasar, domin su bayyana rashin yardar su da abun da suka kira zaben dodo-rido.

Sakamakon farko ya baiwa Mr.Putin kashi 64 cikin dari na kuri’un da aka kada, abokin karawar shi na kurkusa da shi, shugaban jam’iyyar Kwaminis, Gennady Zyuganov kuma kashi 17 cikin dari. Sauran wasu ‘yan takara uku sun kasa da kashi goma-goma cikin dari.

Mr.Putin ya ce ya lashe abun da ya kira “gwagwarmayar gaskiya kuma a bayyane”. Cikin hawaye ya gaisa da dubban daruruwan magoya bayan shi a kofar fadar Kremlin ranar Lahadi, sannan ya yi mu su godiyar hana kasar fadawa hannun abokan gaba masu kokarin yinkwace mulkin, a lafazin shi.

Shugaban kasar Rasha marigayi BorisYeltsin ne ya nada Mr.Putin magajin shi, ranar daya ga watan janairun shekarar dubu biyu. Mr.Putin ya ci zabe daga bisani a wannan shekara sannan ya kara ci a shekarar dubu biyu da hudu. Kundin tsarin mulkin kasar ya haramta mi shi yin wa’adin mulki uku a jere. A shekaru hudun da su ka gabata Mr.Putin ne firai ministan kasar Rasha a karkashin shugaba mai barin gado Dmitry Medvedev.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG