WASHINGTON, D.C. - Trump ya bayyana haka ne a dandalinsa na sada zumunta 'Truth Social", lamarin da ya haifar da tuhumar gwamnatin tarayya da za a iya cewa ita ce bazanar shari’a mafi tsananin da aka yi wa tsohon Shugaban yayin da kuma yake neman komawa fadar White House.
Trump ya ce an bukace shi da ya bayyana a kotun Tarayya ta Miami ranar Talata da karfe uku na yamma. Amma ya ce "BAN AIKATA LAIFI BA" .
Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ba ta yi wani karin bayani ko kuma tabbatar da batun ba a halin yanzu.
Dama mataimakansa suna cikin shiri kan yuwuwar tuhumar shi a binciken bayanan sirri da ake gudanarwa, yayin da aka hango masu gabatar da kara da ke gudanar da binciken a yau Alhamis a wata kotun Miami inda babban alkalai ke sauraron bahasi daga bakin shaidu.
Ku Duba Wannan Ma Kotu Ta Samu Trump Da Laifin Cin Zarafin Wata Mata Ta Hanyar Neman Yin Lalata