Trump ya zama tsohon shugaba Amurka na farko da ya fuskanci tuhume-tuhume a yayin da yake yin takara ta shiga fadar White House, kamar yadda wata majiyar jami’an tsaro ta fada a ranar Alhamis.
Zarge-zargen, da suka taso daga wani bincike karkashin jagorancin lauyan gundumar Manhattan na jam’iyyar Democrat, Alvin Bragg, suna iya sake fasalin takarar shugaban kasa a 2024.
A baya dai Trump ya ce zai ci gaba da yakin neman zaben fitar da gwani na jam’iyyar Republican, idan aka tuhume shi da wani laifi.
Jaridar New York Times ta rawaito cewa, har yanzu dai ba a san takamanman tuhume-tuhumen ba, kuma da alama za a sanar da tuhumar a cikin kwanaki masu zuwa.
Dole Trump ya je zuwa Manhattan don daukar yatsun hannu da sauran abubuwa zuwa wani lokaci.
Nan take dai ofishin Bragg da lauyan da ke wakiltar Trump ba su amsa bukata ta yin magana ba.
Masu taimaka wa alkali yanke hukuci da Bragg ya gayyato a watan Janairu sun fara sauraron shaidu game da rawar da Trump ya taka wajen biyan Daniels kwanaki kafin zaben shugaban kasa na 2016, wanda ya yi nasara.
Daniels, wacce sananniyar jaruma ce a fina-finan batsa kuma darekta, wacce sunanta na gaskiya Stephanie Clifford, ta ce ta karbi kudin ne a madadin ta yi shiru game da saduwa da ta yi da Trump a shekarar 2006.
Tsohon lauyan Trump, Michael Cohen, ya ce Trump ya ba da umarnin biyan kudin toshiyar bakin ga Daniels da kuma mace ta biyu, tsohuwar mai fitowa a fina finan batsa, Karen McDougal, wacce ita ma ta ce tayi muamalar saduwa da Trump. Trump ya musanta cewa yana da alaka da wadannan mata.
Masu gabatar da kara na tarayya sun bincika biyan Daniels a 2018, wanda ya kai ga yanke hukuncin dauri ga Cohen a gidan yari amma babu tuhuma kan Trump.
Babu wani tsohon shugaban Amurka ko mai ci da ya taba fuskantar tuhuma. Har ila yau Trump na fuskantar binciken laifuka guda biyu da wani lauya na musamman da Atoni Janar na Amurka Merrick Garland ya nada da wanda mai gabatar da kara a jihar Georgia ya nada.
A yakin neman zabe na 2024, Trump ya kere abokanan hamayyarsa na farko don zaben fitar da gwani na jam’iyyarsa, inda a kuri’ar jin rayoyi da Reuters/Iposs suka yi ya nuna yana da goyon bayan kashi 43 cikin 100 na ‘yan Republican, idan aka kwatanta da goyon bayan kashi 31 cikin 100 da abokin hamayyar na kusa, Gwamnan jihar Florida, Ron DeSantis, wanda har yanzu bai sanar da takararsa ba. Ana sa ran Biden zai sake neman tsayawa takara.