Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Kwamiti Na Musamman Da Ke Binciken Trump A Georgia Ya Zo Karshe


Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

Kwamitin bincike na musamman a jihar Geogia ta Amurka, da ke binciken ko shugaban kasar na wancan lokacin Donald Trump da abokansa sun aikata wani laifi yayin da suke kokarin juya zaben da ya fadi a shekarar 2020 ya kammala aikinsa.

Alkalin kotun koli na gundumar Fulton, Robert McBurney, wanda ke sa ido kan kwamitin, shine ya ba da umarnin rusa babban kwamitin na musamman a yau Litinin.

Umurnin mai shafi biyu ya ce manyan jami’an sun kammala rahoton karshe, kuma akasarin alkalan kotun sun kada kuri’ar rusa babban kwamitin na musamman.

Kawo karshen aikin kwamitin na musamman ya matsar da binciken matakin kusa da yiwuwar tuhumar Trump da wasu laifuka. Shawarar tuhumar Trump daga rahotan zai kasance ga lauyan gundumar Fulton Fani Willis.

A cikin kusan watanni shida, kwamitin ya saurari shaidu da dama, ciki har da makusantan Trump da dama da kuma wasu manyan jami'an jihar Georgia.

Batun na daga cikin da dama a fadin kasar da ke barazanar fadawa matsalar shari'a ga tsohon shugaban, yayin da yake neman wa'adi na biyu a shekarar 2024.

Jami’an kwamitin na musamman a jihar Geogia ba za su iya gabatar da tuhume-tuhume ba, amma a maimakon haka suna iya fitar da rahoton karshe da zai ba da shawarar abin da yakamata a yi.

XS
SM
MD
LG