Dole Ne ‘Yan Najeriya Su Hada Kai Da Gwamnati Wajen Cimma Manufar Cigabansu - Masana 

Shugaban Najeriya Buhari 

Tawagar aiki na neman samar da cigaban al’umma ta Core Working Group karkashin gwamnatin tarayyar kasar ta yi kira ga ‘yan jaridu da su hada gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki baya ga gwamnati don cimma manufofin ci gaban al’umma a Najeriya.

ABUJA, NIGERIA - A yayin da ake neman mafita mai dorewa a game da batuttuwa da suka shafi ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da kuma uwa-uba bunkasa tattalin arziki a cikin wannan yanayin matsi da Najeriya ke ciki, tawagar aiki na neman samar da cigaban al’umma ta Core Working Group karkashin gwamnatin tarayyar kasar ta yi kira ga ‘yan jaridu da su hada gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki baya ga gwamnati wajen yada manufofin cigaba da ake da su don cimma nasara a kan manufar haɓaka cigaba ga al’ummar kasar.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne a yayin wani taron yin kira ga ‘yan jarida da su hada gwiwa da gwamnati wajen wayar da kan al’umma a game da shiga a dama da su a aikin kawo cigaba da tawagar Core Working Group mai tsare-tsaren cimma manufofin inganta bangaren kiwon lafiya, ilimi, samar da ayyukan yi da dai sauransu ga al’ummar Najeriya da ya gudana a birnin Abuja.

Taron da jagorar CWG, Yosola Akinbi, ta shirya din ya sami halarcin tawagar babban bankin duniya a Najeriya, wakili daga kungiyar gwamnonin kasar, wakilin gidauniyar Bill da Melinda Gates, ofishin kula da raya kasashen waje da na rainon Ingila wato FCDO inda aka tattauna batuttuwan da zasu taimaka wajen kawo sauyin da ake nema a kasar.

Sarah Sambo dake zaman jami’ar tsare-tsare a sakatariyar tawagar aikin CWG, ta ce manufarsu Ita ce tabbatar da cewa an samar da ingantaccen ilimi, kiwon lafiya, aikin yi, bunkasa tattalin arzkin da dai sauransu.

Mamba a kwamitin inganta ayyuka na babban bankin duniya wato enhanced team a turance, Hon. Muhammad Usman, ya bayyana cewa wayar da kan al’umma a yanayin da ake ciki a kasar abu ne mai mahimmancin gaske.

A wani bangare kuwa, mataimakin darakta a gidauniyar Bill da Melinda Gates, Taijjani Muhammad, ya ce bada mahimmanci ga bangaren kiwon lafiya, ilimi, samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa tattalin arziki su ne ababen da za su kawo cigaba a Najeriya.

Shi ma darakta a kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulrazak Bello Barkindo, wanda ya wakilci babban daraktar kungiyar wato Asishana Okauru, ya tofa albarkacin bakinsa a kan wannan batu na kawo ci gaba a kasa.

Manufofin tawagar CWG dai sun hada da wayar da kan ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki a matakai daban-daban a game da ainihin aikin ci gaban ‘yan kasar da abubuwan da ke tattare yin su da kuma fahimtar da su kan dabarun da aka ƙaddamar a kwanakin baya-bayan nan don haɓaka ayyukan ci gaban da aka sa a gaba a Najeriya.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Dole Ne ‘Yan Najeriya Su Hada Kai Da Gwamnati Wajen Cimma Manufar Ci Gabansu - Masana .mp3