Gwamnatin Najeriya dai ta kaddamar da kudin Naira ta yanar gizo don samar da hanyar saukakawa ‘yan kasa wajen hada-hada, amma har yanzu wasu ‘yan kasuwar ba su san yadda tsarin na eNaira ke aiki ba.
Tun bayan kaddamar da wannan kudi na yanar gizo eNaira a watan Oktobar 2021, alamu na nuni da cewa har yanzu ‘yan kasuwa a Najeriya ba su mayar da hankali wajen amfana da wannan sabon shiri ba.
Gwamnatin Najeriya ta kwatanta wannan sabon tsari da Nage Dadi Goma. Sai dai a tattauwar da sashen Hausa ya yi wasu ‘yan kasuwa, mafi yawa na bayyana cewa har yanzu basu san yadda tsarin eNaira yake aiki ba. Tare da kira ga masu ruwa da tsaki su tashi tsaye don wayarwa da al’umma kai.
Duk da yake masana lamuran tattalin arziki na ganin wannan tsarin abu ne mai kyau, wanda ka iya fitar da Najeriya daga kangin wasu matsaloli da ake fama da su. Sai dai rashin wayar da kai daga gwamnati ya sa har yanzu ba a fara ganin moriyar sa ba.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.