Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Shugabanni Sun Yi Adalci, Talaka Ya Gyara Hali, Najeriya Za Ta Zauna Lafiya-Kwararru


Unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters).
Unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters).

Yadda al'amurra ke ci gaba da tabarbarewa a Najeriya ba zai rasa nasaba da kiraye kirayen da shugabanni ke yi ga jama'a akan su nisanci munanan ayyuka ko kasar zata samu fita daga halin kunci, duk yake wasu na ganin suma shugabanni sai sun zamo masu adalci.

Haka zalika wasu kungiyoyi kamar na Hizbah na kan kokarin gyaran halayen jama'a, kamar ta jihar Kebbi wadda ta cika shekaru ashirin tana fafatukar gyaran halayyar jama'ar jihar.

Allah ya albarkaci Najeriya da arziki da yawan jama'a, sai dai kuma kalubale a sassa daban daban na ci gaba da yiwa kasar barazana da kuma tarwatsa lamurranta.

Ko bayan matsalolin rashin tsaro da ke yi wa kasar tarnaki, akwai kuma wasu matsalolin rayuwa da suka haddabi jama'a har ma shugabanni na ganin munanan halayen jama'a ne ke janyo matsalolin don haka akwai bukatar gyara ga munanan halayen.

Kungiyar Hizbah a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin kungiyoyi masu fafstukar gyara munanan halayen jama'a, har a cikin shekaru 20 da ta yi ta samu wasu nasarori kamar yadda kumandan ta Sulaiman Muhammad ya bayyana.

Ya ce barnace-barnace da ake yi a baya kamar wuraren shan giya ko gidan mata yanzu duk sun zamo tarihi, kuma sun sulhunta jama'a akan wasu matsaloli, sun kuma yi kokarin takaita shan miyagun kwayoyi.

Duba da cewa duk wadannan nasarorin jama'a na ci gaba da fuskantar matsalolin rayuwa ya sa shugabanni ke ta kira akan a kara dagewa wajen kamewa daga aikata munanan ayyuka kamar yadda gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu yake kira akai.

Ya ce halaye da dabi'u idan jama'a zasu gudanar da su yadda Allah Ya ce wasu abubuwa da yawa dake aukuwa munana da ba zasu auku ba.

To sai dai masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin ba kira ga jama'a su gyara halaye ne kadai mafita ba, su ma shugabanni akwai bukatar su gyara na su halayen su zama abin koyi ga jama'ar su.

Farfesa Bello Badah mai sharhi ne akan lamurran yau da kullum.

Ya ce “Duk kasar da ake zalunci tsakanin jama'a ko daga shugabanni ba yadda za'a yi kira ya yi tasiri ga jama'a, dole sai kowa ya gyara sa’annan za'a samu zaman lumana”.

A bangaren mabiya addinin kirista ma haka batun yake, idan shugabanni suka zamo adillai jama'a suka gyara halayen su za’a samu saukin rayuwar a cewar malamin kirista Reverend Yakubu Daudu.

Ya ce duk matsalolin da Najeriya ke fuskanta daga mummunan shugabanci ne maras adalci, sauran matsaloli kuwa daga rashin baiwa yara tarbiya ta gari ne.

Fatan ‘yan Najeriya dai ba ta wuce fita daga cikin halin kunci ba, wanda kuma zai samu ne kawai idan aka tafiyar da lamurran cikin adalci.

Ga dai sautin rahoton Muhammad Nasir Daga Sakkwato:

An Gargadi Shugabanni Kan Adalci Da Gyaran Hali Ga Talaka.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG