A Najeriya daidai lokacin da jama'a ke fama da matsalolin rashin tsaro, su kuwa jami'an tsaro kokawa suka yi akan yadda suke samun katsalandam idan suka kama wadanda suke tuhuma da aikata ayyukan ta'addanci lokacin da suke bincikensu.
Wannan na zuwa ne lokacin da ake ta kama wadanda ake tuhumar, duk da yake da wuya a ji hukuncin da ake yi wa wadanda ake kamawar.
Jami'an tsaron Najeriya sun jima suna fitar da sanarwa tare da nuna wadanda suke kamawa da tuhumar aikata ayyukan ta'addanci a sassa daban na kasar duk da yake ba su bayar da bayanan yadda ta kaya bayan gurfanar da wadanda ake tuhuma gaban kuliya.
Duk da yake ayyukan ta'addancin ba tsayawa suka yi ba, amma dai jami'an tsaro na ci gaba da kame wadanda ake tuhuma da hannu ga ayyukan kamar kamar kamen wasu mutane biyar da hukumar tsaron ‘yan kasa ta Civil Defense ta yi a Sokoto wadanda Kwmandan hukumar, Muhammad Sale Dada ya nunawa manema labarai.
A cewarsa, wadanda suka kama sun hada da Abdullahi Dan Hussaini dan shekara 45 wanda shi ne shugaban barayin duk da yake ya musanta shi ne shugabansu, amma sauran akan aikinsa da aka kama sun tabbatar da shi ne jagoransu wanda ke kiran masu garkuwa da mutane daga wasu wurare suna zuwa Sokoto suna aika-aikarsu.
Sai dai matsalar da ke nan ita ce katsalandam da jami'an ke fuskanta daga sassa daban na neman afuwa ga wadanda ake kamawar lokacin da ake bincikensu, kamar yadda kwmandan hukumar ya koka akai.
A cewar Dada, akwai wasu da suke neman su yi katsalandam ga aikin bincike musamman na Dan Hussaini, kuma bincike ya nuna dangin Dan Hussaini sun yi alkawalin bayar da kudi miliyoyi don a kashe batun, har da amfani da lauyoyi amma dai wannan ba zai hana su aikinsu bisa doka ba.
Duk da yake jama'a na kallon yawan kama wadanda ake tuhuma da laifi a zaman kokarin jami'an tsaro, masana lamurran tsaro na ganin da saura saboda jami'an ba su bayar da bayanan ko an kama wadanda ake tuhumar ta laifi an hukumta su ko akasin haka.
Dokta Yahuza Ahmad Getso na ganin cewa ya kamata hukumomi su rinka baiwa jama'a bayanai akan ire-iren hukuncin da ake yi wa wadanda suke gurfanarwa gaban kuliya.
A cewar Dr. Yahuza, sau da yawa ana kai masu laifi gidan gyara hali su kwashe shekaru 25 ko 30 ba a yanke musu hukunci ba, wannan zai ci gaba da karfafawa masu aikata laifuka cewa Najeriya wuri ne da kowa zai iya cin karenshi ba babbaka.
Don haka ya ce ya kamata mahukunta su rika tauna tsakuwa domin bai wa aya tsoro.
Masanan dai na ganin muddin ana hukunta masu laifi yadda ya kamata zai zama izna ga masu son aikata irin wannan laifin a gaba.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto: