Da Dan Gari: Tarihin Garin Tsauri, Katsina

A shirin Da Dan Gari na wannan makon gidan rediyon Vision FM Katsina ya kai ziyara garin Tsauri da ke karamar hukumar Kurfi a jihar Katsina a Najeriya don jin takaitaccen tarihin garin.

Gidado I Abdullahi, shine Maigarin Tsauri, ya ce garin na Tsauri wanda aka kafa a shekarar 1840 ya taba zama gari na biyu a daraja a masarautar Katsina kuma garin ya shahara a fannin ilimi da yaki a zamanin bayan. Hausawa, Fulani, da Bare-bari sune kabilun da aka sani a garin a cewarsa.

Basaraken ya kuma ce asalin sunan garin "Sauki" amma daga baya ya koma "Tsauri."

Saurari cikakken shirin wanda Abdurrahaman Kabir Jani ya gabatar.

Your browser doesn’t support HTML5

Da Dan Gari: Tarihin Garin Tsauri, Katsina