Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Bin Bahasin Zargin Rundunar SARS Ya Fara Aiki


Suleiman Galadima
Suleiman Galadima

Kwamitin bincike mai zaman kansa akan zargin cin zarafin da rundunar SARS ta aikata ya fara aiki.

Kwamiti mai zaman kansa da hukumar kare hakkin bil’adama wato NHRC ta kafa ya fara zama domin sauraron kararraki a yau 4 ga watan Nuwamba, a kan korafe-korafen cin zarrafi, tare da wuce gona da iri a yayin gudanar da aiki da ake zargin rusasshen sashin ‘yan sanda na SARS da aikatawa a baya. A halin yanzu kwamitin ya karbi kararraki sama da 160 a Birnin Tarayya, Abuja.

Babban jojin kotun ayyukan kwadago, mai ritaya Suleiman Galadima, ya yi bayani a kan fara zaman kwamitin sauraron korafe-korafen cin zarrafi, da ake zargin rusasshen sashen rundunar ‘yan sandan na SARS da su. "Yanzu mun fara sauraron korafe korafen, zamu hada rahotonmu don mika wa gwamnatin tarayya. Bayanan suna da matukar muhimanci."

Kakakin majalisar matasan Najeriya, Mubarak Mijinyawa da ya halarci zaman kwamitin mai zaman kansa na farko, ya bayyana gamsuwarsa da tsarin kwamitin. "Kawo yanzu dai mun gamsu da yadda aikin kwamitin yake gudana, wanda sai da ta kaimu daga muryoyinmu kamun aka kai inda ake yanzu."

A bangaren wadanda suka shigar da kara, Frank Ugbaji, daga jihar Cross River, ya ce ya fuskanci cin zaraffi mai tsanani a hannun jami'an SARS, a lokacin da aka kai karar batar wasu kaya daga Otel din da ya ke aiki a Delta, yana kan aiki aka gayyace su zuwa caji ofis din 'yan sandan jihar.

Jami’an sun masa tambayoyi a kan kayan, kuma ya bayyana mu su cewa ba shi da masaniya, aka kama shi tare da mai da shi sashin SARS na unguwar Garki a birnin Abuja tare da daure kafafunsa da hannu jikin wani katako, a juye kansa na tsawon fiye da sa’o’i uku, kuma yana neman a masa adalci.

Shi ma Mr Bello Akugbioku mazaunin Abuja, ya bayyana cewa alburushin ‘yan sanda ya same shi a lokacin zanga-zangar 'yan Shi’a a gaban shelkwatar rundunar ‘yan sanda ta Abuja.

An dai fara samun korafe-korafen cin zarrafi da ake zargin rundunar ta SARS da aikatawa tun daga shekarar 2017, bayan wani matashi mai suna Segun Awosanya ya fara gwagwarmayar neman a kawo karshen SARS a kafaffen sada zumunta, sakamakon zarginsu da kisan gilla, cin zarrafin al’umma, kame-kame ba bu gaira ba dalili, karbar rashawa, yin lalata da yara mata da dai sauran su.

Ga rahoton da Halima Abdulra’uf ta aiko muna a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG