A wani taron kara wa juna sani da hukumar Kwastan reshen jihar Lagos da kuma masu ruwa da tsaki wajen kiwon kaji da kuma lafiya ta gudanar anan birnin Lagos, sun bayyana bukatar mutane su kiyaye da cin kajin da ake shigowa dasuu daga kasashen waje, wadanda aka rigaya aka sarrafa.
A cewar babban kwanturolan hukumar ta kwastan reshen jihar Lagos, Alhaji Turaki Usman yace hukumar ta dukufa wajen hana shigowa da kajin da aka sarrafa su daga kasashen ketare a bisa shawaran jamiaan kiwon lafiya abinda yasa hukumar kamawa da kuma lalata irin wadannan kaji na kasashen ketare da ake shigowa dasu.
"Baya da wani abu sai dai ma yasa maka wasu cuta babu wani maganar lafiya a ciki ka ga duk ire-iren wadannan abubuwan sai ya kara zaburar damu muka ce to yakamata mu hada kai dasu wadannan mutane muga cewa mun cimma burin mu, amma gaskiyan Magana yana da yawa, yana da yawa ba dan kadan ba, yana da yawa sosai mun lalata katan yakai dubu goma sha wani abu’’
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba kungiyar masu kiwon kaji ta kasa kokawa tayi game da rashin biyan cikakken diyya ga yayan kungiyar da gonakin su a can baya aka rufe sabila da kamuwa da cutar murar tsuntsaye da akasarin kajin kasar suka yi.
Abinda kuma sakataren kungiyar na kasa Alhaji Abubakar Babagana yace idan dai gwamnati bata dauki mataki na biyan diyya ba to ko shakka babu matakan da take son ta dauka na ganin an inganta kiwon kaji a cikin gida yana cike da matsaloli da dama.
‘’Akwai wasu lokaci da suka wuce wadanda jihohi da dama akwai masu kiwon kaji wadanda aka zo aka ce cutar zazzabin tsuntsaye (Bird Flu) din nan ya shigo akan a kashe kajin nan aka kona su, aka kashe wanda har yanzu gwamnati bata yi musu wani abu akai ba, to kaga kuwa yanzu idan dai ana so aci gaba da yin haka, datsewa da akayi wannan yayi dai-dai, to amma kuma a sake samun wadannan mutanen a basu goyon baya sai mu samu mujtanen da zasu yi mana kiwon kaji din sosai domin nan din ta wadata a Najeriya ya zamana ako ina akwai kajin duk wanda yake da shaawan kajin ya zamana akwai shi anan gida ba sai an dinga kawo na waje ba’’
Yanzu dai babban gargadi da hukumomin lafiya keyi na cin kajin da ake shigowa dasu daga kasashen waje bayan an sarrafa su shine na kamuwa da cutar kansa (CANCER) ko daji ko sa kiba a sabili da sinadarai da ake saka musu da ke hana su lalacewa wuri kamar yadda wata jamiaar kiwon lafiya da kuma kula da abinci mai gina jiki Malama Hadiza Karu ta shaida wa muryar Amurka.
‘’Naman kazan nan ina son in sanar ma jamaa da cewa akan barshi cikin akwatin sanyi ya dade to idan ya dade yawacin anfanin dake cikin wannan naman baya ciki kuma ga dan adam, ga lokacin da dana dam yaci’’
Ga Babangida Jibrin da Karin bayani daga birnin Ikko.
Your browser doesn’t support HTML5