Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Carolina Ta Kudu Ta Sauko Da Tutar 'Yan Aware Daga Ginin Majalisa


Bakar fata da wasu masu adawa da kafa wannan tuta ta jihohin da suka nemi ballewa daga Amurka a lokacin yakin basasa, sun fi shekaru 20 su na gwagwarmayar neman ganin an kawar da ita saboda alamun da take nunawa na wariyar launin fata.

Washington, DC -- Wata tawagar 'yan sandan sintiri a kan hanya ta Jihar Carolina ta Kudu a Amurka, ta sauko da tutar jihohin da suka nemi ballewa daga Amurka a lokacin yakin basasa, wadda kuma aka kafa a cikin harabar majalisar dokokin jihar fiye da shekaru 50 da suka shige.

Wannan matakin yazo makonni uku a bayan kisan kare-dangi na kyamar launin fatar da aka yi ma wasu bakaken fata su 9 cikin cocinsu a Charleston, babban birnin jihar Carolina ta Kudu.

Daruruwan mutane, jinsuna dabam-dabam, sun taru suna bayyana farin ciki da murna, tare da kirarin sunan Amurka "USA, USA" a yau jumma'a a yayin da ake saukar da wannan tuta daga harabar majalisar, abinda mutane da yawa a jihar suka yi tsammanin cewa ba zai taba faruwa ba.

Da yawa daga cikin sun tafi dauke da tutar Amurka a hannunsu.

A kofar shiga majalisar, mutanen dake goyon bayan cire wannan tuta sun ninka wadanda suka je domin nuna fusatar cirewar da aka yi. Wani dan majalisa bakar fata ya fadawa gidan telebijin na CNN cewa shi da sauran 'yan raji sun shafe shekaru fiye da 20 suna gwagwarmaya da kauracewa cibiyoyin jihar a kokarin neman cire wannan tuta.

'Yan wasa da mawaka da dama sun ki yin wasa a jihar Carolina ta Kudu a saboda wannan batu na kafa tutar a harabar majalisa.

An cire wannan tutar kwana daya a bayan da gwamnar jihar, Nikki Haley, ta sanya hannu a kan dokar da 'yan Democrat da Republican suka zartas a majalisa kan cire wannan tuta ta zamanin yakin basasa.

Ita dai wannan tuta, ita ce tutar wasu jihohin Amurka, cikinsu har da ita Carolina ta Kudu wadanda suka balle daga Amurka a shekarun 1860 a saboda ba su goyi bayan haramta bauta ba.

Masu adawa da tutar suna bayyana ta a zaman alama ta nuna fifikon farar fata da kuma bautar da bakar fata.

Masu goyon bayan barinta sun ce alama ce ta tarihi da kuma alfahari ga 'yan jihohin. Da yawa daga cikinsu sun ce suna kyamar 'yan wariyar launin fatar da suka saci wannan tuta a zaman alamarsu.

XS
SM
MD
LG