Babban Bankin Najeriya (cbn) ya rage yawan harajin bada kariya ga intanet a hada-hada ta na’ura daga kaso 0.5% zuwa kaso 0.005% cikin 100 a sabon jadawalinsa na harkokin kudin na shekarar 2024 zuwa 2025.
“CBN zai ci gaba da tursasa biyan harajin dole na kaso 0.005 cikin 100 a kan dukkanin cinikayyar da bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi suka yi ta na’ura, a cewar dokar yaki da laifuffukan intanet, ta 2015.”
Harajin, wanda aka gabatar karkashin dokar yaki da laifuffukan intanet ta 2015, wacce aka sabunta a 2024, an kirkire shi ne domin tallafawa asusun yaki da laifuffukan intanet na kasa, da ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro ke gudanar da shi
Ku Duba Wannan Ma CBN Ya Umarci Bankuna Su Caji Kashi 0.5 Cikin 100 A Matsayin Harajin Tsaron Intanet Ku Duba Wannan Ma Tinubu Ya Dakatar Da Aiwatar Da Dokar Harajin Yanar GizoZa’a caji kaso 0.005 cikin 100 a kan dukkanin cinikayyar da bankunan kasuwanci dana hada-hada tsakanin kamfanoni da bankunan da basa mu’amala da kudin ruwa da hada-hadar kudi ta na’ura da sauransu.