A yau Alhamis, Mambobin Majalisar Wailan Najeriya suka bukaci babban bankin kasar wato CBN ya janye sanarwar daya fitar wacce ke umartar bankuna su fara aiwatar da shirin cirar harajin rabin kaso 1 cikin 100 na kudaden da aka tura ta na’ura, inda suka bayyanata a matsayin “me cike da rudani”
A cewar Majalisar Wakilan, dole ne CBN ya janye sanarwar daya fitar tunda fari, tare da maye gurbinta da wacce babu rudani a cikinta.
Dan Majalisa Kingsley Chinda ya ja hankalin majalisar akan tawili da dama na umarnin babban bankin wadanda suka ci karo da ainihin fassarar ayoyin dokar tsaron intanet din.
Akan haka majalisar ta bayyana damuwar cewa, za’a aiwatar da dokar a kuskure matukar ba a dauki matakan gaggawa, na warware matsalollin dake tattare da umarnin CBN da kuma dokar tsaron intanet din ba.
A ranar 6 ga watan Mayun da muke ciki, CBN ya fitar da sanarwar dake umartar ilahirin bankunan Najeriya da cibiyoyin hada-hadar kudi na tafi da gidanka dama dukkanin masu sana’ar biyan kudade dasu fara cirar sabon harajin tsaron intanet, sakamakon ka’idojin da aka zayyana a cikin dokar yaki da lafuffukan yanar gizo ta Najeriya da aka yiwa gyaran fuska a bana.
A cewar dokar, za’a tattara tare da tura harajin rabin kaso 1 cikin 100 na kudaden da aka tura ta na’ura zuwa ga asusun tara kudaden tsaron intanet na kasa, wanda ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro zai rika sa ido akai.
Dandalin Mu Tattauna